Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 20:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Duka biyu suka ruga a guje, amma almajirin nan ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin.

5. Yana duƙawa yana leƙa ciki, sai ya ga likkafanin lilin a ajiye, amma fa bai shiga ba.

6. Sa'an nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye,

7. mayanin kuma da yake kansa ba a ajiye tare da likkafanin yake ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya.

8. Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya.

9. Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa lalle ne yă tashi daga matattu.

10. Sai almajiran suka koma gida.

11. Maryamu kuwa tana tsaye a bakin kabarin daga waje, tana kuka. Tana cikin kuka sai ta duƙa, ta leƙa kabarin,

12. sai ta ga mala'iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu.

13. Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.”

14. Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba.

15. Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.”

Karanta cikakken babi Yah 20