Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 19:19-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.”

20. Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci.

21. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus, “Kada ka rubuta ‘Sarkin Yahudawa’, sai dai ka rubuta, ‘A faÉ—arsa shi ne Sarkin Yahudawa.’ ”

Karanta cikakken babi Yah 19