Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 16:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.

9. Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba,

10. a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.

11. a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.

12. “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba.

13. Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku.

14. Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.

15. Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”

16. “Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.”

17. Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?”

Karanta cikakken babi Yah 16