Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 16:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe.

2. Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi.

3. Za su yi haka ne kuwa domin ba su san Uba ko ni ba.

4. Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku.

5. Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’

6. Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku.

7. Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.

8. Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.

9. Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba,

10. a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.

11. a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.

12. “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba.

Karanta cikakken babi Yah 16