Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 15:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.

17. Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”

18. In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku.

19. Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.

20. Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, ‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma.

21. Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba.

22. Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu.

23. Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma.

24. Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka.

25. An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’

26. Amma sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni.

27. Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.

Karanta cikakken babi Yah 15