Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 15:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa.

14. Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku.

15. Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.

16. Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.

17. Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”

18. In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku.

19. Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.

20. Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, ‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma.

21. Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba.

22. Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu.

Karanta cikakken babi Yah 15