Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 11:38-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin.

39. Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Sai Marta, 'yar'uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.”

40. Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?”

41. Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.

42. Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama'ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.”

43. Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!”

44. Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuska tasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”

45. Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi.

46. Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi.

47. Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka?

48. In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.”

49. Amma ɗayansu, wai shi Kayafa, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba.

50. Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a, da duk jama'a ta halaka.”

51. Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama'a,

52. ba ma saboda jama'a kaɗai ba, har ma yă tattaro 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina su zama ɗaya.

Karanta cikakken babi Yah 11