Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 10:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, 'yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba.

9. Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.

10. Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

11. Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.

12. Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran.

13. Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin.

14. Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,

15. kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin.

16. Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda.

17. Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma.

18. Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”

19. Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa.

20. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”

Karanta cikakken babi Yah 10