Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 10:23-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. damuna ce kuma, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali,

24. sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.”

25. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata.

26. Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina.

27. Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.

28. Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

29. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban.

30. Ni da Uba ɗaya muke.”

31. Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu su jajjefe shi.

32. Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?”

33. Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.”

34. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?

35. To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi),

36. kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?

37. In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.

38. Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”

39. Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.

40. Sa'an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can,

41. mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu'ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”

Karanta cikakken babi Yah 10