Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 1:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah.

3. Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.

4. Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.

5. Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.

6. Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya.

7. Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa.

8. Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

9. Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.

10. Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba.

11. Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba.

12. Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah,

13. wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.

14. Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.

15. Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ”

Karanta cikakken babi Yah 1