Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 9:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mala'ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga wani tauraron da ya faɗa a kan duniya daga sama, aka ba shi mabuɗin ramin mahallaka.

2. Ya kuwa buɗe ramin mahallakar, sai wani hayaƙi kamar na babbar matoya ya taso, har hayaƙin ramin nan ya duhunta rana da sararin sama.

3. Fāri suka fito zuwa cikin duniya daga cikin hayaƙin nan, aka ba su ikon harbi, irin na kunamin duniya.

4. Aka kuwa hana su cutar ciyayin duniya, ko tsiro, ko kowane itace, sai dai mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu.

5. Aka kuwa yardar musu su yi musu azaba har wata biyar, amma kada su kashe su, azabarsu kuwa, kamar ta kunama take, in ta harbi mutum.

6. A waɗannan kwanaki kuwa mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba, za su ƙagauta su mutu, mutuwa kuwa sai ta guje musu.

7. Kamannin fārin nan kuwa kamar dawakai ne da suka ja dāgar yaƙi, a kansu kuma da wani abu kamar kambin zinariya, fuskarsu kuwa kamar ta mutum,

8. gashinsu kamar na mace, haƙorinsu kuma kamar na zaki.

9. Suna saye da sulkuna kamar na ƙarfe, dirin fikafikansu kuwa kamar dirin kekunan doki masu yawa ne suna rugawa fagyan yaƙi,

10. wutsiyarsu kamar ta kunama, ga kuma ƙari, ikonsu yana ji wa mutane ciwo har wata biyar kuwa a wutsiyarsu yake.

11. Sarkinsu kuwa da yake iko da su shi ne mala'ikan mahallaka, sunansa da Yahudanci Abadan, da Helenanci kuwa Afoliyon.

Karanta cikakken babi W. Yah 9