Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 7:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai na ga wani mala'ika yana hawa daga mafitar rana, riƙe da hatimin Allah Rayayye. Sai ya yi wa mala'ikun nan huɗu magana da murya mai ƙarfi, waɗanda aka bai wa ikon azabtar da ƙasa da teku,

3. yana cewa, “Kada ku azabtar da ƙasa, ko teku, ko itatuwa, sai mun buga wa bayin Allahnmu hatimi a goshinsu tukuna.”

4. Sai na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba'in da huɗu ne, daga kowace kabilar Isra'ila,

5. wato, an yi wa dubu goma sha biyu hatimi daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad,

6. dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa,

Karanta cikakken babi W. Yah 7