Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 3:16-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. To, saboda kai tsakatsaki ne, ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi, zan tofar da kai daga bakina.

17. Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma.

18. Saboda haka, ina yi maka shawara ka sayi zinariya a guna, wadda aka tace da wuta, don ka arzuta, da kuma fararen tufafi da za ka yi sutura, ka rufe tsiraicinka don kada ka ji kunya, da kuma man shafawa a ido don ka sami gani.

19. Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.

20. Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.

21. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.

22. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

Karanta cikakken babi W. Yah 3