Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 17:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Amma mala'ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan buɗa maka asirin matar nan, da kuma na dabbar nan mai kawuna bakwai, da ƙaho goma, da take ɗauke da ita.

8. Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo.

9. Fahimtar wannan abu kuwa, sai a game da hikima. Wato, kawuna bakwai ɗin nan tuddai ne guda bakwai, waɗanda matar take a zaune a kai.

10. Har wa yau kuma, sarakuna ne guda bakwai, waɗanda biyar daga cikinsu aka tuɓe, ɗaya yana nan, ɗayan bai zo ba tukuna, sa'ad da ya zo kuwa, lalle zamaninsa na lokaci kaɗan ne kawai.

11. Dabbar da take nan dā, a yanzu kuwa ba ta, ita ce ta takwas, daga cikin bakwai ɗin nan kuma ta fito, za ta kuwa hallaka.

12. Ƙahonin nan goma kuwa da ka gani, sarakuna goma ne, waɗanda ba a naɗa ba tukuna, amma sa'a ɗaya tak, za a ba su ikon yin mulki tare da dabbar.

13. Waɗannan ra'ayinsu ɗaya ne, za su kuma bai wa dabbar nan ikonsu da sarautarsu.

14. Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”

Karanta cikakken babi W. Yah 17