Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 16:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai na ji wata murya mai ƙara daga Haikalin, tana ce wa mala'ikun nan bakwai, “Ku je ku juye tasoshin nan bakwai na fushin Allah a kan duniya.”

2. Daga nan mala'ikan farko ya je ya juye abin da yake a tasarsa a kan duniya, sai kuwa waɗansu mugayen miyaku masu azabtarwa suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar nan, suke kuma yi wa siffarta sujada.

3. Mala'ika na biyu ya juye abin da yake a tasarsa a teku, ya zama kamar jinin mataccen mutum, kowane abu mai rai na cikin teku kuma ya mutu.

4. Mala'ika na uku ya juye abin da yake a tasarsa a koguna da maɓuɓɓugan ruwa, sai suka zama jini.

5. Na kuwa ji mala'ikan ruwa yana cewa,“Kai mai adalci ne a hukuncin nan naka,Ya kai Mai Tsarki, wanda kake a yanzu, kake kuma a dā.

Karanta cikakken babi W. Yah 16