Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 1:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. A tsakiyar fitilun nan kuwa, na ga wani kamar Ɗan Mutum, saye da riga har idon sawu, ƙirjinsa kuma da ɗamarar zinariya.

14. Kansa da gashinsa farare fat ne kamar farin ulu, farare fat kamar alli, idanunsa kamar harshen wuta,

15. ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar wadda aka tace a maƙera, muryarsa kuma kamar ƙugin ruwaye masu gudu.

16. Yana riƙe da tauraro bakwai a hannunsa na dama, daga bakinsa kuma takobi mai kaifi biyu yake fitowa. Fuskarsa tana haske kamar rana a tsaka.

17. Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,

18. ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.

19. To, ka rubuta abubuwan da ka gani, da abubuwan da suke a nan a yanzu, da abubuwan da suke shirin aukuwa bayan wannan.

20. Asirtacciyar ma'anar taurarin nan bakwai da ka gani a hannuna na dama kuwa, da kuma fitilun nan bakwai na zinariya, to, su taurarin nan bakwai, mala'iku ne na ikilisiyoyin nan bakwai, fitilun nan bakwai kuwa, ikkilisiya bakwai ɗin ne.

Karanta cikakken babi W. Yah 1