Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Tit 1:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Shaidar nan tasa kuwa gaskiya ce. Saboda haka, dai ka tsawata musu da gaske, domin su zama sahihai a wajen bangaskiya,

14. a maimakon su mai da hankali ga almarar Yahudawa, ko kuwa dokokin mutane masu ƙin gaskiya.

15. Ga masu tsarkin rai duk al'amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al'amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.

16. Suna cewa sun san Allah, amma suna sāɓa masa ta wurin aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani a wajen yin aiki nagari.

Karanta cikakken babi Tit 1