Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Tit 1:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu,

2. duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil'azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,

3. ya kuwa bayyana maganarsa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa'azin da shi Allah Mai Cetonmu ya amince mini in yi, bisa ga umarninsa,

4. zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka.Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.

5. Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al'amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikkilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka,

6. sai wanda ya kasance marar abin zargi, mai mace ɗaya, wanda 'ya'yansa suke masu ba da gaskiya, waɗanda ba a zarginsu da aikin masha'a ko na kangara.

Karanta cikakken babi Tit 1