Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 6:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Mutuwar nan da ya yi kuwa, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari, saboda shafe zunubanmu, amma rayuwar da yake yi, yana rayuwa ne, rayuwa ga Allah.

11. Haka ku ma sai ku lasafta kanku kamar ku matattu ne ga zunubi, amma kuna a raye rayuwa ga Allah, ta wurin Almasihu Yesu.

12. Saboda haka, kada ku yarda zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha'awarsa.

13. Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.

14. Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari'a take iko da ku ba alherin Allah ne.

15. To, ƙaƙa? Wato, sai mu yi zunubi don shari'a ba ta iko da mu, sai alherin Allah? A'a, ko kusa!

16. Ba ku sani ba, shi wanda kuke miƙa kanku a gare shi domin yi wa biyayya, lalle ku bayi ne na wanda kuke yi wa biyayya ɗin (ko bautar zunubi wanda ƙarshensa mutuwa ne, ko bautar biyayya wadda ƙarshenta adalci ce)?

17. Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku.

18. Da aka 'yanta ku kuma daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin adalci.

19. Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.

20. Sa'ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.

21. To, wace fa'ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne.

Karanta cikakken babi Rom 6