Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 5:8-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma kuwa Allah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.

9. To, tun da yake a yanzu an kuɓutar da mu ta wurin jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan.

10. In kuwa tun muna maƙiyan Allah aka sulhunta mu da shi ta mutuwar Ɗansa, to, da yake an sulhunta mu, ashe kuwa, za a fi kāre mu ta wurin rayuwarsa ke nan.

11. Banda haka ma, har muna fariya da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami sulhun nan a yanzu.

12. To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi.

13. Lalle fa zunubi yana nan a duniya tun ba a ba da Shari'a ba, sai dai inda ba shari'a, ba a lasafta zunubi.

14. Duk da haka kuwa mutuwa ta mallaka tun daga Adamu har ya zuwa Musa, har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi irin na keta umarnin da adamu ya yi ba, wanda yake shi ne kwatancin mai zuwan nan.

Karanta cikakken babi Rom 5