Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 4:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Saboda haka al'amarin ya dogara ga bangaskiya, domin yă zama bisa ga alheri, don kuma a tabbatar da alkawarin nan ga dukkan zuriyar Ibrahim, ba ga masu bin Shari'a kaɗai a cikinsu ba, har ma ga waɗanda suke da bangaskiya irin Ibrahim, shi da yake ubanmu duka.

17. kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na sa ka uban al'ummai da yawa.” Shi ne kuwa ubanmu a gaban Allah, wannan da ya gaskata, wato mai raya matattu, shi ne kuma mai kiran marasa kasancewa kamar sun kasance.

18. Ibrahim kuwa ko da yake ba halin sa zuciya a gare shi, sai ya yi ta sawa, ya gaskata zai zama uban al'ummai da yawa, kamar yadda aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za ta yawaita.”

19. Bangaskiyarsa kuwa ba ta raunana ba, bai dubi gajiyawar jikinsa ba, don yana da shekara wajen ɗari a lokacin, ko kuma cewa Saratu ta wuce haihuwa.

20. Ba kuwa wata rashin bangaskiyar da ta sa shi shakkar cikar alkawarin Allah, sai ma ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa ya yi, yana ɗaukaka Allah,

21. yana haƙƙaƙewa, cewa Allah na da ikon yin abin da ya yi alkawari.

22. Shi ya sa aka lasafta bangaskiyarsa adalci ce a gare shi.

23. To, “lasafta masa” ɗin nan da aka rubuta kuwa, ba saboda Ibrahim kaɗai aka rubuta ba,

24. har saboda mu ma, za a lasafta mana, wato mu da muke gaskatawa da wannan da ya ta da Yesu Ubangijinmu daga matattu,

25. wanda aka bayar a kashe saboda laifofinmu, aka kuma tashe shi, domin mu sami kuɓuta ga Allah.

Karanta cikakken babi Rom 4