Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 2:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi.

2. Mun dai san hukuncin Allah a kan masu yin haka daidai ne.

3. Ya kai mutum, kai da kake ganin laifin masu yin haka, alhali kuwa kai kanka, kana yinsu, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?

4. Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba?

5. Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.

6. Allah ne zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa.

7. Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami.

8. Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda suke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala.

9. Duk waɗanda suke aikata mugunta za su sha wahala da masifa, da fari Yahudawa, sa'an nan kuma al'ummai.

10. Amma Allah zai ba da daraja, da ɗaukaka, da salama ga dukan waɗanda suke aikata nagarta, da fari ga Yahudawa, sa'an nan ga al'ummai.

11. Domin kuwa, Allah ba ya nuna tara.

Karanta cikakken babi Rom 2