Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 8:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, sai in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”

10. Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.

11. Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a Mulkin Sama,

12. 'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”

13. Sai Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka, ya zama maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.

14. Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzaɓi.

15. Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.

16. Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu aljannu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljannun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

17. Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”

18. To, da Yesu ya ga taro masu yawan gaske sun kewaye shi, sai ya yi umarni a koma wancan hayi.

Karanta cikakken babi Mat 8