Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 8:24-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci.

25. Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”

26. Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!

27. Mutanen suka yi al'ajabi, suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska da ruwan teku ma suke masa biyayya?”

28. Da ya isa wancan hayi a ƙasar Garasinawa, mutum biyu masu aljannu suka fito daga makabarta suka tarye shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya.

29. Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”

30. Nesa kuma kaɗan akwai wani babban garken alade na kiwo.

31. Sai aljannun suka roƙe shi, suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladen nan.”

32. Ya ce musu, “To, ku je.” Sai suka fita, suka shiga aladen. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka hallaka a ruwa.

33. Masu kiwon aladen suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin kome da kome, da kuma abin da ya auku ga masu aljannun.

34. Sai ga duk jama'ar garin sun firfito su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.

Karanta cikakken babi Mat 8