Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 8:15-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.

16. Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu aljannu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljannun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

17. Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”

18. To, da Yesu ya ga taro masu yawan gaske sun kewaye shi, sai ya yi umarni a koma wancan hayi.

19. Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”

20. Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

21. Sai ɗaya daga almajiran ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”

22. Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu.”

23. Da ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi.

24. Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci.

25. Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”

26. Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!

27. Mutanen suka yi al'ajabi, suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska da ruwan teku ma suke masa biyayya?”

28. Da ya isa wancan hayi a ƙasar Garasinawa, mutum biyu masu aljannu suka fito daga makabarta suka tarye shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya.

29. Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”

30. Nesa kuma kaɗan akwai wani babban garken alade na kiwo.

Karanta cikakken babi Mat 8