Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 8:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawan gaske suka bi shi.

2. Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.”

3. Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke.

4. Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

5. Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani jarumi ya zo gunsa ya roƙe shi,

6. ya ce, “Ya Ubangiji, yarona na kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.”

7. Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”

8. Sai jarumin, ya ce, “Ya Ubangiji, ban isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke.

9. Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, sai in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”

Karanta cikakken babi Mat 8