Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 5:4-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.

5. “Albarka tā tabbata ga masu tawali'u, domin za su gāji duniya.

6. “Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.

7. “Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.

8. “Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.

9. “Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.

10. “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.

11. “Albarka tā tabbata gare ku sa'ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.

12. Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”

13. “Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.

14. “Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa.

15. Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa'an nan ta ba duk mutanen gida haske.

16. To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”

Karanta cikakken babi Mat 5