Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 3:16-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan da ya fito daga ruwan, sai ga sama ta dāre, ya ga Ruhun Allah na saukowa kamar kurciya, har ya sauka kansa.

17. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.”

Karanta cikakken babi Mat 3