1. A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya,
2. yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”
3. Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce,“Muryar mai kira a jeji yana cewa,‘Ku shirya wa Ubangiji tafarki,Ku miĆ™e hanyoyinsa.’ ”