Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:60-66 Littafi Mai Tsarki (HAU)

60. ya sa shi a wani sabon kabari da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi.

61. Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.

62. Kashegari, wato, bayan ranar shiri, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus,

63. suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.

64. Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa'an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.”

65. Sai Bilatus ya ce musu, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare shi iyakar ƙoƙarinku.

66. Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka buga wa dutsen nan hatimi, suka kuma sa sojan tsaro.

Karanta cikakken babi Mat 27