Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.”

12. Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa, bai ce kome ba.

13. Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da suke ba da shaida a kanka ba?”

14. Amma bai ba shi wata amsa, ko da ta kalma ɗaya ba, har mai mulki ya yi mamaki ƙwarai.

15. To, a lokacin idi kuwa mai mulki ya saba sakar wa jama'a kowane ɗaurarre guda da suka so.

16. A lokacin kuwa da wani shahararren ɗan sarƙa, mai suna Barabbas.

17. Da suka taru sai Bilatus ya ce musu, “Wa kuke so in sakar muku? Barabbas ko kuwa Yesu da ake kira Almasihu?”

18. Don ya sani saboda hassada ne suka bashe shi.

19. Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari'a, sai mata tasa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha'anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkinsa.”

20. To, sai manyan firistoci da shugabanni suka rarrashi jama'a su zaɓi Barabbas, Yesu kuwa a kashe shi.

21. Sai mai mulki ya sāke ce musu, “Wane ne a cikin biyun nan kuke so in sakar muku?” Sai suka ce, “Barabbas.”

22. Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!”

23. Ya ce, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara ɗaga murya suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi!”

Karanta cikakken babi Mat 27