Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 26:62-75 Littafi Mai Tsarki (HAU)

62. Sai babban firist ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”

63. Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”

64. Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”

65. Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!

66. Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya cancanci kisa!”

67. Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi,

68. suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”

69. To, Bitrus kuwa yana zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya a kansa, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu Bagalile!”

70. Amma ya musa a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da kike nufi ba.”

71. Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!”

72. Sai ya sāke musawa har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.”

73. Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.”

74. Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara.

75. Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

Karanta cikakken babi Mat 26