Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 26:55-71 Littafi Mai Tsarki (HAU)

55. Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.

56. Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

57. Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafa, babban firist, inda malaman Attaura da shugabanni suke tare.

58. Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin.

59. To, sai manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi.

60. Amma ba su samu ba, ko da yake masu shaidar zur da yawa sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso,

61. suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.”

62. Sai babban firist ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”

63. Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”

64. Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”

65. Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!

66. Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya cancanci kisa!”

67. Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi,

68. suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”

69. To, Bitrus kuwa yana zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya a kansa, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu Bagalile!”

70. Amma ya musa a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da kike nufi ba.”

71. Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!”

Karanta cikakken babi Mat 26