Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 26:45-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi, kuna hutawa? To, ga shi, lokaci ya yi kusa. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.

46. Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni nan, ya matso!”

47. Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.

48. To, mai bashe shi ɗin ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi.”

49. Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa.

50. Yesu ya ce masa, “Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?” Suka matso suka ɗanke Yesu, suka kama shi.

51. Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunne.

52. Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zare takobi, takobi ne ajalinsa.

53. Kuna tsammani ba ni da ikon neman taimako gun Ubana ba, nan da nan kuwa ya aiko mini fiye da rundunar mala'iku goma sha biyu?

54. To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?”

Karanta cikakken babi Mat 26