Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 26:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗi azurfa talatin, suka ba shi.

16. Tun daga lokacin nan ne ya riƙa neman hanyar da zai bashe shi.

17. To, a ranar farko ta idin abinci marar yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina kake so mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”

18. Sai ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce lokacinsa ya yi kusa, zai ci Idin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’ ”

19. Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Idin Ƙetarewa.

20. Da magariba ta yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu.

21. Suna cikin cin abinci, sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

22. Sai suka yi baƙin ciki gaya, suka fara ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne, ya Ubangiji?”

Karanta cikakken babi Mat 26