Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 26:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce wa almajiransa,

2. “Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”

3. Sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa.

4. Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi.

5. Amma suka ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kada jama'a su yi hargitsi.”

6. To, sa'ad da Yesu yake Betanya a gidan Saminu kuturu,

7. sai wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tandu na man ƙanshi mai tsadar gaske, ta tsiyaye masa a kā, a lokacin da yake cin abinci.

8. Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!

9. Da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba gajiyayyu!”

10. Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.

11. Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.

12. Zuba man nan da ta yi a jikina, ta yi shi ne domin tanadin jana'izata.

13. Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharar nan a duniya duka, abin da matar nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

14. Sai ɗaya daga cikin sha biyun nan, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci,

15. ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗi azurfa talatin, suka ba shi.

Karanta cikakken babi Mat 26