Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 24:30-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.

31. Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”

32. “Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan.

33. Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake.

34. Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.

35. Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

36. “Amma fa wannan rana da wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da yake Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.

37. Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.

38. Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi,

39. ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.

40. A sa'an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

41. Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

42. To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.

43. Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.

44. Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”

Karanta cikakken babi Mat 24