Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 24:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yesu ya fita Haikalin, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo suka nuna masa gine-ginen Haikalin.

2. Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”

3. Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”

4. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku,

5. domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa.

6. Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jitajitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna.

7. Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar ƙasa a wurare dabam dabam.

8. Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.

9. “Sa'an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al'ummai za su ƙi ku saboda sunana.

10. A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.

11. Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.

12. Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi.

Karanta cikakken babi Mat 24