Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 20:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma'aikata don aikin garkarsa ta inabi.

2. Da ya yi lada da su a kan dinari guda a yini, sai ya tura su garkarsa.

3. Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga waɗansu suna zaman banza a bakin kasuwa.

4. Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku abin da yake daidai.’ Sai suka tafi.

5. Da ya sāke fita wajen tsakar rana, da kuma azahar, ya sāke yin haka dai.

6. Wajen la'asar kuma ya fita ya sami waɗansu a tsaitsaye, ya ce musu, ‘Don me kuke zaman banza yini zubur?’

7. Sai suka ce masa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata.’

Karanta cikakken babi Mat 20