Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 2:2-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.”

3. Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.

4. Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Attaura na jama'a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu.

5. Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,

6. ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza,Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba,Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki,Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”

7. Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana.

8. Sa'an nan ya aike su Baitalami, ya ce, “Ku je ku binciko mini ɗan yaron nan sosai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada.”

9. Su kuwa da suka ji maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda ɗan yaron nan yake.

10. Da suka ga tauraron sai suka yi matuƙar farin ciki.

11. Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.

12. Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.

13. Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”

14. Yusufu kuwa ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da uwa tasa da daddare, ya tafi Masar,

Karanta cikakken babi Mat 2