Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 18:28-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’

29. Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, ai, zan biya ka.’

30. Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, har yā biya bashin.

31. Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana.

32. Sai ubangiji nasa ya kira shi, ya ce masa, ‘Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni,

33. ashe, bai kyautu kai ma ka ji tausayin abokin bautarka, kamar yadda na ji tausayinka ba?’

34. Ubangijinsa ya yi fushi, ya ba da shi ga masu azabtarwa har yă biya duk bashin da ake binsa.

35. Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa 'yan'uwanku da zuciya ɗaya ba.”

Karanta cikakken babi Mat 18