Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 15:33-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?”

34. Yesu ya ce musu, “Gurasa nawa suke gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da ƙananan kifaye kaɗan.”

35. Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa.

36. Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a.

37. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.

38. Waɗanda suka ci kuwa maza dubu huɗu ne, banda mata da yara.

39. Da ya sallami taron ya shiga jirgi ya tafi ƙasar Magadan.

Karanta cikakken babi Mat 15