Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”