Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 15:23-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana binmu tana cika mana kunne da kuka.”

24. Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.”

25. Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!”

26. Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.”

27. Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”

28. Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'ya tata ta warke.

29. Yesu ya tashi daga nan, ya bi ta bakin Tekun Galili. Sai ya hau dutse ya zauna a can.

30. Taro masu yawan gaske suka zo wurinsa, suka zazzo da guragu, da masu dungu, da makafi, da bebaye, da kuma waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa, ya kuwa warkar da su.

31. Har jama'ar suka yi ta al'ajabi da ganin bebaye suna magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu na tafiya, makafi kuma suna gani, duk suka ɗaukaka Allah na Isra'ila.

32. Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”

33. Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?”

34. Yesu ya ce musu, “Gurasa nawa suke gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da ƙananan kifaye kaɗan.”

35. Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa.

36. Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a.

37. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.

Karanta cikakken babi Mat 15