Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 14:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ko da yake yana son kashe shi, yana jin tsoron jama'a, don sun ɗauka shi annabi ne.

6. To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,

7. har ma ya yi mata rantsuwa zai ba ta duk abin da ta roƙa.

8. Amma da uwa tasa ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.”

9. Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.

10. Ya aika aka fille wa Yahaya kai a kurkuku,

11. aka kuwa kawo kan a cikin akushi, aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa uwa tasa.

12. Almajiransa suka zo suka ɗauki gangar jikin, suka binne, suka kuma je suka gaya wa Yesu.

13. Da Yesu ya ji haka sai ya tashi daga nan, ya shiga jirgi zuwa wani wuri inda ba kowa, domin ya kaɗaita. Amma da taron jama'a suka ji haka, suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa.

14. Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.

15. Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”

16. Yesu ya ce, “Ba lalle su tafi ba. Ku ku ba su abinci mana.”

17. Sai suka ce masa, “Ai, gurasa biyar da kifi biyu kawai muke da su a nan.”

Karanta cikakken babi Mat 14