Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 14:19-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a.

20. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu.

21. Waɗanda suka ci kuwa misalin maza dubu biyar ne banda mata da yara.

22. Sai ya sa almajiransa suka shiga jirgi su riga shi hayewa kafin ya sallami taron.

23. Bayan ya sallami taron, ya hau dutse shi kaɗai domin ya yi addu'a. Har magariba ta yi yana can shi kaɗai.

24. Sa'an nan kuwa jirgin yana tsakiyar teku, raƙuman ruwa mangara tasa, gama iska tana gāba da su.

25. Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun.

Karanta cikakken babi Mat 14