Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 13:8-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin.

9. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

10. Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa kake musu magana da misalai?”

11. Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.

12. Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

13. Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.

14. Lalle a kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,Za ku kuma gani, amma ba za ku gane ba faufau,

15. Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta,Sun toshe kunnuwansu,Sun kuma runtse idanunsu,Don kada su gani da idanunsu,Su kuma ji da kunnuwansu,Su kuma fahimta a zuciyarsu,Har su juyo gare ni in warkar da su.’

16. Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.

17. Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.

18. “To, ga ma'anar misalin mai shukar nan.

19. Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.

20. Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki.

21. Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe.

Karanta cikakken babi Mat 13