Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 13:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.

18. “To, ga ma'anar misalin mai shukar nan.

19. Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.

20. Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki.

21. Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe.

22. Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.

23. Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”

24. Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa.

25. Sa'ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa.

26. Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana.

27. Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’

28. Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Bayin suka ce masa, ‘To, kana so mu je mu cire mu tara ta?’

29. Amma ya ce, ‘A'a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma.

Karanta cikakken babi Mat 13