Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 12:39-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Sai ya amsa musu ya ce, “'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama! Amma ba wata alama da za a nuna musu sai dai ta Annabi Yunusa.

40. Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.

41. A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.

42. A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta kā da su, don ta zo ne daga bangon duniya ta ji hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.

43. “Baƙin aljan in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa neman hutu, amma ba ya samu.

44. Sa'an nan sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ Sa'ad da kuwa ya koma, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacce.

45. Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”

46. Yana cikin magana da taro, sai ga Uwa tasa da 'yan'uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi.

47. Wani ya ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”

48. Sai ya amsa wa wanda ya gaya masa, ya ce, “Wace ce tsohuwata, su wane ne kuma 'yan'uwana?”

49. Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa, ya ce, “Ga nan tsohuwata da 'yan'uwana nan!

50. Ai, kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so, shi ne ɗan'uwana, shi ne 'yar'uwata, shi ne kuma tsohuwata.”

Karanta cikakken babi Mat 12