Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 11:13-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Domin dukan annabawa da Attaura sun yi annabci har ya zuwa kan Yahaya.

14. In kuma za ku karɓa, shi ne Iliya da dā ma zai zo.

15. Duk mai kunnen ji, yă ji.

16. “To, da me zan kwatanta zamanin nan? Kamar yara ne da suke zaune a kasuwa, suna kiran abokan wasansu, suna cewa,

17. ‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba!’

18. “Ga shi, Yahaya ya zo, ya ƙi ciye-ciye da shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da iska.’

19. Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”

20. Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al'ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba.

21. “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.

22. Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.

23. Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.

24. Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Saduma a kanki.”

25. A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.

26. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.

27. Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa.

28. Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.

Karanta cikakken babi Mat 11